16 Satumba 2020 - 15:24
Japan : An Nada Yoshihide Suga, A Matsayin Sabon Firaminista

A Japan, an nada Yoshihide Suga, a matsayin sabon firaminista wanda zai maye gurbin firaministan kasar mai murabus Shinzo Abe.

ABNA24 : Nan gaba a yau Laraba ne ake sa ran zai firaministan zai sanar da sabbin mambobin gwamnatinsa.

Dan shakaru 71, Mista Suga, ya kasance na hannun daman tsohon firaminista Shinzo Abe, wanda ya yi murabus saboda dalilai na rashin lafiya.

A ranar Litini data gabata ne, Yoshihide Suga, ya lashe zaben cikin gida na jam’iyyar (PLD), wanda ya bashi damar zama firayi minista.

Yayin jawabin amincewa da zabensa da jam’iyyarsa ta yi, Yoshihide Suga, ya sha alwashin ci gaba da manufofin firaminista mai barin gado Abe, da zummar shawo kan matsalolin da ke addabar al’ummar kasar.

342/